Monday 19 January 2026 - 21:45
Ta'aziyyar Ayatullah A'arafi ga Ayatullahil Uzma Sistaniy 

Hauza/ Shugaban makarantun ilmin addinin Musulunci (Hauza) ya mika ta'aziyyarsa ta rasuwar Ayatullah Hajj Sayyid Hadi Sistaniy, dan uwan mai girma Ayatullah Sistaniy.

A cewar rahoton Ofishin Yada Labaran Hauza, rubutun sakon ta'aziyyar Ayatullah A'arafi ga shi kamar haka:

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Innalillahi wa inna ilaihir raji'un

Rashin babban Mallami mai daraja Ayatullah Hajj Sayyid Hadi Sistaniy bayan rayuwa mai cike da kokari da mujahadar ilimi da aiki abu ne da ya bar tarihi.

Ina mika sakon ta'aziyyata na rashin wannan Mallami mai daraja ga mai girma babban marja'i, Ayatullah Sayyid Ali Sistaniy, sauran iyalan da ya bari, gidajen da rashin ya shafa da kuma manyan dalibansa. Ina rokon Allah (SWT) ya gafarta masa kuma ya daukaka makwancinsa. Ina kuma rokon Allah ya bawa iyalansa ladan juriya da hakurin wannan babban rashi.

Alireza A'arafi

Shugaban Makarantun Hauza

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha